Tunatarwa da jan hankalin shugabanin rassan hukumar zabe na sassan kasa akan maganar mutunta dokokin zabe, a yayin zabukan da ake shirin gudanarwa a karshen shekarar nan ta 2020, shine makasudin wannan taro na tsawon kwanaki 2, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar zabe Dr Aladoua Amada ya bayyana.
Jami’ai sama da 300 da ke da alhakin tafiyar da sha’anin zabe ne ke halartar wannan taron. Shugabar hukumar zabe ta jihar Dosso Me Aicha Garba na cewa za su kiyaye dukkan bayanan da suka ji daga shugaban hukumar na kasa. Shugabar hukumar zabe ta jihar Dosso, Me Aicha Garba ta bayyana cewa za su kiyaye dukkan bayanan da suka ji daga shugaban hukumar na kasa.
A na sa bangaren shugaban reshen CENI na gundumar Inates da ke yankin Tilabery, Abdoul Aziz Mahamadou, ya yi kira da cewar ‘yan kasa su maida hankalinsu akan wannan zaben, yayin da ya bukaci hukumar zabe ta tanadi wadatattun kayan aiki da suka kamata, a kuma isar da su akan lokaci.
A yanzu haka hukumar ta na gab da kammala aikin samar da katin zabe, wanda za a fara rabon shi nan bada jimawa ba, da kuma hanyoyin da suka kamata a bi wajen rabonsu ba tare da wata matsala ba.
Tsarin jaddawalin hukumar zabe ya yi nuni da cewa, a ranar 13 ga watan Disambar da ke tafe, za a gudanar da zaben kananan hukumomi, yayin da za a gudanar da zaben ‘yan-majalisun dokoki da zagayen farko na zaben shugaban kasa a ranar 27 ga watan na Disamba.
A saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti.
Facebook Forum