Wasu mayakan sa kai sun kai mummunan hari akan barikin sojin saman kasar India a kusa da kan iyakar Pakistan, inda hakan ya haifar da bata kashin sa’o’i 15 tsakaninsu da sojin gwamnati.
Rundunar sojojin India a tankokin yaki da jirgin sama mai saukar Ungulu ne suka kai musu daukin da aka murkushe maharani. Jami’ai sun ce mutane 7 suka mutu gaba daya wanda 5 sune maharan.
Har yanzu dai jami’an India sunce suna kokarin gano ko su waye maharan. Sai dai jami’an tsaron kasar sun ce suna da yakinin mayakan nan ne da ake wa lakabi da Jeish-e-Mohammed, wato sojojin Mohammed. Wato mayakan da ke fafutukar neman ‘yancin yankin Kashmir. Amma gwamnatin Islamabad ta musanta zargin.
Ministan cikin gidan Indiya yace, “Pakistan makwabtanmu ne kuma muna son zaman lafiya tsakaninmu, ba ma su ba, har kasashen da muke makwabtaka da su. In ‘yan ta’addar suna kai mana hari, zamu basu amsa daidai da su”.