Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan ‘yan bindigar, kuma shugaban shirin afuwar gwamnatin kasar Birgediya Janal Paul Boroh mai Ritaya, yace an sami wani tsaiko ne na biyan tsofaffin ‘yan bindigar yankin Niger Delta, sakamakon matsin tattalin arzikin da kasar Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ranar Talata 2 ga wannan wata na Agusta ne gwamnatin Najeriya ta ci gaba da biyan kudaden alawus alawus na N65000 ga wakonne ‘dan bindiga dake cikin shirin afuwar gwamnatin Najeriya. baya ga biyansu kudaden, shirin ya tanadi horar da tsofaffin ‘yan bindigar domin kawo karshen kai hare hare a sassa daban daban kan bututun Mai a yankin.
Bayanai dai na nuna cewa gwamnatin Najeriya na da niyyar kawo karshen shirin afuwar gwamntin kasar ga ‘yan bindigar na Niger Delta nan da shekaru biyu masu zuwa, haka nan kuma gwamnatin zata fito da wani shiri na a koma gona ga ‘yan bindigar na yankin Niger Delta.
Domin karin bayani.