‘Yan sandan Brazil sun ce sun damke wani madugun fataken muggan kwayoyi da yayi kaurin suna, wanda aka shafe shekaru 30 ana farautarsa.
Hukumomi suka ce Luiz Carlos da Rocha, yaje likitoci sun sauya masa kamanni a yunkurinsa na kaucewa shiga hannu.
Jami’ai sun yi imanin cewa da Rocha, wanda ya sauya sunansa zuwa Vitor Luiz de Moraes, shine madugun wata kungiyar fataucin hodar iblis ta Cocaine mai rassa a kasashe da dama.
Hukumomi suka ce ana fataucin hodar iblis ta Cocaine da shi wannan madugun da kungiyarsa suke sarrafawa cikin kurmin kasashen Bolivia da Colombia da kuma Peru, zuwa kasashen Turai da kuma nan Amurka. Jami’ai suka ce da Rocha yana daya daga cikin manyan masu samarwa da muggan dillalan kwayoyi na biranen Sao Paulo da Rio de Janeiro, hodar iblis ta Cocaine da suke sayarwa.
‘Yan sanda sun kama kadarorin da Rocha na dalar Amurka miliyan 10, ciki har da motocin alatu, da jirgin sama, da gonaki da wasu gine-ginen. Amma kuma ‘yan sandan sun yi Imani da cewa yana da kadarorin da suka kai akalla dala miliyan 100, kuma zasu farauto su a zagaye na biyu na binciken madugun fataucin kwayoyin.
Facebook Forum