Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar da ta sami goyon bayan dukkan mambobinta a jiya alhamis, na rage ayyukan wanzar da zaman lafiya da ake gudanarwa a yankin Darfur na kasar Somaliya da kimanin kashi 30 cikin 100.
Kudurin da Birtaniya ta gabatar ya sami asali ne bisa la’akkari da ingancin harkokin tsaro da aka samu a Darfur, da kuma matsin lambar Majalisar Dinkin Duniya ta ke fuskanta daga Amurka, wadda ta bukaci a rage dala miliyan 600 daga ayyukan wanzar da zaman lafiya da Majalisar ta ke gudanarwa.
An shafe kimanin shekaru 15 ana fama da matsaloli a yankin Darfur tun bayan wani rikicin kabilanci da ya barke na adawa da gwamnati, wanda ya haifar da maida martanin sojijin gwamnati, tare da goyon bayan ‘yan tawayen kasashen larabawa.
An kashe kimanin mutane dubu 300, sama da miliyan biyu kuma suka kauracewa matsugunansu.
Kamfan ruwa da kuma yunwa sun kara asassa wahalar da suke fuskanta.
Facebook Forum