Kafofin yada labaran Syria da kungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights dake Birtaniya, sun ce motocin bas-bas sun kwashi mutane dubu uku daga garuruwan Foua da Kfarya, wadanda suka koma hanun gwamnati.
A can baya yankunan suna hanun mayakan ‘yan tawaye ne.
Baya ga haka wasu motocin bas din sun yi jigilar daruruwan mutane daga yankunan Madaya da Zabadani dake hanun ‘yan tawayen, wadanda dakarun dake marawa gwamnati baya suka yi wa kawanya.
Wannan shiri na kwashe jama’ar garuruwan a yankunan, na karkashin wata matsaya da aka cimma a watan da ya gabata.
Harin bam din da aka kai ranar Asabar a yankin Rashideen, wanda ya fada kan wasu motocin bas-basa da suka yi jerin gwano dauke da mutanen dake goyon bayan gwamnati, ya kashe mafi yawan mutanen da ake kwashewa.
Kwamitin Sulhu na Majaliasar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, inda ya kwatanta harin a matsayin wani abin “rashin imani da ragwanci.”
Facebook Forum