An bude cibiya ta farko ta kula da matan da aka yi musu fyade ko aka ci musu zarafi a asibitin Umaru Shehu dake Maiduguri a Jihar Borno, domin kula da irin wadannan mata da aka yi kiyasin cewa a duk fadin Najeriya, babu inda suke da yawa kamar a Jihar Borno.
Hajiya Nana Kashim Shettima, uwargidan gwamnan Jihar Borno, ita ce ta kaddamar da wannan cibiya wadda aka gina tare da tallafin Hukumar Al'adu da Ilmi ta kasar Britaniya, watau British Council.
Hajiya Nana ta ce wannan matsala ta fyade da cin zarafin mata ta fi yawaita a Jihar Borno a saboda fitinar Boko Haram, da kuma yadda miliyoyin mutane ala tilas suka kaura daga gidaje da garuruwansu.
Kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Borno, Dr. Haruna Mshelia, yace koda yake kashi casa'in da takwas cikin 100 na mutanen da ake cin zarafinsu mata ne, kada a mance da sauran kashi daya ko biyu na mazan da su ma suka shiga cikin irin wannan ukuba. Su ma ya kamata a ba su damar halartar wannan cibiya a duk lokacin da suka samu kansu cikin irin wannan yanayi.
Wani likitan da ya gabatar da jawabi a wajen taron yace wata kididdigar da Hukumar Kiwon Nlafiya ta Duniya ta gudanar ta nuna cewa kashi daya cikin uku na mata sukan fuskanci fyade ko cin zarafi a rayuwarsu.
Yace ya zuwa shekarar 2014, an gano cewa yawan yin fyade wa mata ya karu sosai ta yadda ya zamo a cikin mata biyar, to guda daya an taba yi mata fyade.
Facebook Forum