Wannan rahoto da hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a kwanannan na zargin kungiyar ‘yan tawayen kasar ta People’s Liberation Army in Opposition ko kuma SPLA-IO, da sace mutane dari tara da kuma tilastawa wasu dubu 24 suka arce daga gidajensu a jihar Western Equatorial, tsakanin watannin Afrilu da Agusta. A daidai wannan lokaci ne kuma bangarori masu gaba da junan a Sudan ta Kudu suke tattaunawa a kan sake duban yarjejeniyar zaman lafiya.
Rahoton ya kuma zargi dakarun gwamnati da kashe fararen hula da lalata kadarorinsu. Masu magana da yawun dukkan bangarorin sun musunta cewa dakarunsu suna kashe fararen hula.
Elizabeth Throssell itace jami’a mai kula da harkokin yada labarai a hukumar kare hakkin bil adama ta MDD. Ta fadawa wata ma'aikaciyar radiyon Majalisar Dinkin Duniya Miriya cewa rahoton ya bayyana irin yawan tashin hankali da aka yi a yankin Western Equatorial.
Facebook Forum