Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAJERIYA: An Kaddamar Da Dakin Tattara Bayanan Cin Zarafin Mata a Abuja


Dakin sa ido da tattara bayanan cin zarafin mata.
Dakin sa ido da tattara bayanan cin zarafin mata.

Mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta bayyana cewa, har yanzu akwai gagarumin aiki a gaba a kokarin shawo kan cin zarafin mata a kasashen duniya.

Mataimakiyar sakatariyar ta bayyana haka ne a jawabinta yayin kaddamar da wata cibiyar tattara bayanai da sa ido kan cin zarafin mata da aka kafa a ma’aikatar harkokin mata ta tarayyar Najeriya.

Bisa ga cewarta, kalubale da mata ke fuskanta iri daya ne a kasashen Afrika sai dai kawai wasu lokuta sukan sake kama amma illar su daya ce.

mahaifiyar-yarinyar-da-mutum-7-suka-yi-wa-fyade-ta-nemi-gwamnati-ta-bi-mata-kadi

lauyoyi-mata-sun-jajirce-don-yakar-cin-zarafin-mata-da-yara-a-najeriya

matasa-uku-sun-yi-wa-yar-shekaru-13-fyade-tare-da-kasheta-a-jihar-katsina

Mataimakiyar sakatariyar ta ce babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya tura su zuwa kasashe domin bibiyar matsalolin da suke addabar kasashen da nufin neman hanyoyin shawo kansu. Ta ce tawagarta ta kai ziyara a kasashen Najeriya, Nijar, Ghana, Saliyo da kuma Mali inda suka tarar kowacce kasa tana fama da wani abu da ya sha wa mata kai dangane da kalubale da mata da kananan yara su ke fuskanta.

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Dauniya, Amina Mohammed
Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Dauniya, Amina Mohammed

Tace "abinda zan iya cewa shi ne a dukan kasashen nan, cin zarafin mata na iya zuwa ta wani salo dabam, amma ya yi kamari ainun, abinda ka ke tararwa ke nan a kasashen Afrika, abinda kuma ke faruwa ke nan a kasashen duniya. Mun kuma yadda annobar CODVID19 ta kara sa lamarin ya tsananta, a wadansu wurare ma, suka ninka har sau uku."

Ta ce a har yanzu ana fuskantar kalubalen aurar da kananan yara da wuri a Jamhuriyar Nijar. duk da ci gaba da ake samu a cimma gurin muradun karni da kari, har yanzu mata suna ci gaba da fuskantar kalubale.

Ta kuma bayyana cewa, kashi tamanin cikin dari na matan Saliyo, suna fama da matsalar yi wa mata kaciya. A Mali kuma inda ake fuskantar sauyin mulki, mata har yanzu suna fuskantar rayuwa inda ake kuntata masu a cikin gidaje ko kuma a wuraren da ake gudanar da ayyukan jinkai. A Ghana inda ake shirin gudanar da zabe, nan ma ana cin zarafin mata.

Dakin sa ido da tattara bayanan cin zarafin mata
Dakin sa ido da tattara bayanan cin zarafin mata

Ta ce sun taru a ma’aikatar harkokin matan ta tarayyar Najeriya domin jan hankali kan cin zarafin mata da kuma daukar matakin kawo karshen shi. Bisa ga cewar Amina Mohammed, ana iya shawo kan wannan matsalar, ba domin mata sun ce za a iya ba, amma domin abu ne mai yiwuwa.

Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga ‘yan majalisa da shugabannin al’umma da suka halarci taron su kai wannan sakon a jihohi da kananan humumi da mazabunsu domin ganin an cimma wannan burin.

Tun farko a jawabinta, ministar ma’aikatar harkokin mata, Pauline Tallen ta bayyana cewa, sun bude dakin tattara bayanan ne domin samar da dama ga matan da basu da hanyar tuntubar wani su kai kukansu kai tsaye domin a san halin da suke ciki a kuma nemi hanyar taimaka masu. Ta kuma bayyana muhimmancin wannan dakin tare da yin kira ga maza su bada gudummuwa domin haka ta cimma ruwa.

Ministar harkokokin mata, Pouline Tallen
Ministar harkokokin mata, Pouline Tallen

Za a rika tattara bayanan cin zarafin mata a duk fadin kasar tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi da jihohi. Za a yi taswirarsu yadda mutum zai iya ganin adadin matan da aka ci zarafinsu a kowanne mataki da irin yanayin da suka fuskanta da adadin wadanda suka tagayyara ko kuma rasa rayukansu sakamakon cin zarafinsu, da matakan da aka dauka da dai sauran muhimman bayanai da suka shafi cin zarafin mata.

Daga watan Satumba zuwa 18 ga watan Nuwamba da aka kaddamar da dakin, a sami rahoton cin zarafin mata dubu biyu a jiha guda, wadanda daga ciki biyar suka rasa rayukansu sakamakon munin lamarin.

Bukin kaddamar da dakin sa ido da tattara bayanan cin zarafin mata
Bukin kaddamar da dakin sa ido da tattara bayanan cin zarafin mata

Banda kaddamar da wannan dakin, an kuma karrama maza da suka dauki alkawarin tsayawa mata da kuma jajircewa wajen ganin an kawo karshen cin zarafinsu. An kuma mikawa babbar bakuwar kyauta a madadin matan Najeriya domin nuna goyon bayan aikin ta take yi.

Taron ya sami halartar ministoci, ‘yan majalisun tarayya, jami’an diplomasiya, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

An Kaddamar Da Dakin Tattara Bayanan Cin Zarafin Mata a Abuja-6:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:01 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG