Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Takaddama Kan Makomar Dunkulewar Najeriya


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Tun bayan zanga zangar EndSARS batun makomar dunkulewar Najeriya a matsayin kasa daya al'umma daya ya sake zama wani abin takaddama. Yayin da wasu ke ganin kamata ya yi a raba, wasu na ganin rigimar rabawar ta ma fi matsalar zama tare muni.

An dade ana kai ruwa rana a game da kiraye-kirayen a sake fasalta Najeriya ko kuma a raba kasar kowa ya san inda dare ya masa, kuma a baya-bayan nan kiraye-kirayen na kara samun karbuwa, inda wasu ‘yan kasar kama daga wasu jami'an gwamnati, ‘yan siyasa, masu fada a ji, ‘yan kasuwa, matasa ke nuna goyon bayansu ga batun, lamarin da ke haddasa rarrabuwar kawuna. Wasu na fafutukar a raba kasar, wasu kuma na da burin Najeriya ta cigaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya.

Alal misali, a yayin da wasu ‘yan aware a Najeriya ke nacewa cewa a raba kasar, wasu kuma na ta bayyana goyon bayansu a kan kasar ta cigaba da zama dunkulalliya, hade da batun neman a sake fasalta ta,

To ko menene makomar Najeriya a matsayin kasa daya? Alkalin Alkalai na jihar Katsina mai ritaya kuma tsohon Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyya, Isa Muhammad Dododo, ya bayyana cewa Turawa sun yi shinfida mai kyau na gina Najeriya kuma wadanda su ka gaji Turawan sun yi koyi da su. Ya ce tun bayan da aka kashe mutanen farko aka shigo da wasu irin tsare tsare masu illa ga kasar.

Nigeria
Nigeria

Kiraye-kirayen baya-bayan nan dai ba sa rasa nasaba da raunin gwamnatin kasar ta fuskar wayar da kan al’umma a kan ayyukan ta, kamar yadda fitaccen lauya Barista Mainasara Kogo ya ce Shugabannin siyasan yanzu ba su ilimantar da 'yan Najeriya wajen sanin muhimmancin zaman kasar dunkulalliya. Ya kuma ce kamata ya yi mutane sun kula da abin da za su tarar bayan barin duniya saboda marasa karfi su samu adalci.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zuru/Fakai/Danko-Wasagu/Sakaba na jihar Kebbi a tarayyar Najeriya, hon. Kabir Ibrahim Tukura, ya ce duk da cewa ana bukatar gyare-gyare ta fuskoki daban-daban a kasar, akwai hikima a tattare da Najeriya ta cigaba da zama a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kano a kan zuba jari a kasashen waje, malama Hama Ali Aware, ta tofa albarkacin bakinta a kan wannan batun da cewa ana amfana da juna a zaman taren.

Shi ma shugaban kungiyar bada tallafi na Ford, Dr. Kole Shattima, ya ce kiraye-kirayen a raba kasar ba shi ne maganin matsalolin da suka addabi al’umma ba.

A baya-bayan nan dai, kungiyoyin fafutuka da dama na ta yin kira a kan a sake fasalta Najeriya inda wasu yan aware ke neman a raba kasar ta hanyar gudanar da zanga-zanga lamarin da ya dada sanya fargaba a zukatan ‘yan kasar musamman a wannan lokaci da duniya ke fuskantar matsalolin tattalin arziki sakamakon tasirin annobar Korona birus.

A wani bangare kuma, mawallafin jaridar yanar gizo na Neptune Prime, Alh. Hassan Gimba, ya ce yanayin da kasa ke ciki ne musababbin kiraye-kirayen raba ta. Ya ce idan aka kyautata abubuwa a kasar za a daina jin duriyar masu neman kawo fitina.

Masana a fannin zamantakewar dan adam dai sun ce kamata gwamnati ta mayar da hankali a kan abubuwan da ke haddasa wannan kiraye-kirayen domin samo mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

A tarihin tarayyar Najeriya, tun bayan samun yancin cin gashin kai, ba sabon abu ba ne a samu masu fafutukar neman ballewa daga kasar, musamman idan aka yi la’akari da dimbin al’ummominta, banbancin yanayi, fadin kasa, baiwar albarkatun kasa, bunkasar ilimi, zamantakewa da kumatattalin arziki.

Ga Halima Abdulra’uf da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:06 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG