Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Sojojin Zimbabwe Manyan Mukamai


Wasu manyan sojojin Zimbabwe a lokacin bikin rantsar da shugaba Emmerson Mnangagwa
Wasu manyan sojojin Zimbabwe a lokacin bikin rantsar da shugaba Emmerson Mnangagwa

Sojoji a Zimbabwe sun kwashe manyan mukamai a sabuwar gwamnatin da Emmerson Mnangagwa ya kafa bayan da aka tursasa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya yi murabus.

Sabon shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya nada manyan jami’an sojin kasar a wasu muhimman mukamai.

A jiya Alhamis aka fitar da sanarwar a gidan talbijin din kasar.

Ba a dai zabi ko daya daga cikin bangaren ‘yan adawa ba a mukamai 22 da ke majalisar zartawar sabuwar gwamnatin.

Hakan kuma ya kawar da zaton da ake na cewa Mnangagwa zai fi tsohon shugaban kasar Mugabe tafiya da kowa da kowa.

A makon da ya gabata, Mugabe mai shekaru 93 ya yi murabus daga mukaminsa a kasar ta Zimbabwe, wacce ke kudancin Afirka, bayan da ya fuskanci matsin lamba, inda ya kwashe shekaru 37 yana mulki.

Sojojin kasar ne suka fara kawar da Mugabe, lamarin da ya kai ga har ya rasa goyon bayan majalisar dokokin kasar da ke da mafi rinjayen ‘yan jam’iyar ZANU-PF mai mulki.

Sabusio Moyo, wanda shi ne Janar din ya shiga kafar talbijin ya sanar da karbe mulki daga hannun Mugabe, ya zama sabon Ministan harkokin wajen kasar ta Zimbabwe.

An kuma nada Perence Shiri wanda da shi ne shugaban rundunar sojin saman kasar a matsayin Ministan harkar noma da kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG