Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Kotu A Kasar Zimbabwe Tace Karbe Mulki Da Sojoji Suka Yi Ba Juyin Mulki Bane


ZIMBABWE -- Emmerson Mnangagwa speaks after being sworn in as Zimbabwe's president in Harare, November 24, 2017
ZIMBABWE -- Emmerson Mnangagwa speaks after being sworn in as Zimbabwe's president in Harare, November 24, 2017

Babban kotu a kasar Zimbabwe tace karbe mulki da sojoji kasar suka yi ba juyin mulki bane, kotun tace sojojin sun bayyana cewa sunyi haka domin kar wadanda ke kusa da shugaban da bai kamata su karbe mulkin ba suyi hakan.

Babban kotu a kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yau asabar cewa karbe mulkin da sojoji sukayi wanda yayi dalilin saukar tsohon shugaban kasar Roberty Mugabe daga kan karagar mulki ba abu ne da bai sabawa doka ba, illa shawarar ce da sojoji suka yanke wanda suka ce ba juyin mulki bane.

Kotu tace sojojin sunce sunyi haka ne domin guje wa wasu dake kusa da tsohon shugaban su karbe mulki ba bisa tsarin zabe ba , suna gudanar da ayyukan shugaban kasa wanda hakan ko ba dai-dai bane.

Kotu ta fitar da wannan bayanin ko, kwana daya bayan an rantsad da sabon shugaban kasar shekaru kussan arbain rabon da kasar ta samu wani sabon shugaba, wanda kuma yayi alkawarin kawo sauye-sauyen tattalin arzikin kasar da ya dade cikin mawuyacin hali.

Shugaba Emerson Mnangagwa ya fara aiki ne daga jiya jumaa bayan an rantsad dashi,a kasar data kwashe shekaru 37 karkashin mulkin kama karya na shugaba Robert Mugabe wanda ya sauka ranar talatar data gabata bayan matsi lambar da yasha daga sojoji dama jamiyyar su mai mulkin kasar.

A cikin jawabin sa jim kadan da karban ragamar mulkin kasar Mnangagwa yace zai kokarta ganin gwamnatin ta Zimbabwe ta biya basussukar da ake binta na kasashen waje, kana zata yi sassauci ga shigo da kayayyaki,kana zata yi sauki wajen ganin ‘yan kasar sun samu damar mallakar kudaden waje, wannan kalamai nasa ya sa murna ga zukatar ‘ya kasar domin ko kasa ce data dade tana anfani da kusan kudade kala daban-daban har tara.

Haka kuma yayi alkawarin biyan diyya ga mutanen da aka anshe gonakin su a lokacin mulkin shugaba Mugabe

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG