Amurka tana shirin bukin cika shekaru dari da haihuwar tsohon shugaban kasar Ronald Reagan, wanda ya yi wa’adi biyu na mulki cikin shekara ta dubu da dari tara da tamanin, wanda kuma ake dauka a matsayin shugaban kasar Amurka da yafi kwarjini. Mr. Reagan ya rasu cikin shekara ta dubu biyu da hudu yana da shekaru casa'in da uku a duniya, zai kuma cika shekaru dari da haihuwa gobe lahadi. Ana karrama Mr. Reagan dan jam’iyar Republican a bukukuwa da dama da ake gudanarwa a fadin kasar, tsohon shugaban kasar ya jagoranci abinda ake kira juyi juyin halin masu ra’ayin mazan jiya a matsayin shugaban kasa, ana kuma daukarshi a matsayin gwarzon iya Magana. Ana yabawa Mr. Regan domin taimakawa wajen kawo karshen yakin cacar baki da kungiyar Soviet, da farfado da tattalin arzikin Amurka da ya tabarbare, da kuma zaburar da Amurkawa su zama da kyakkyawar fata. Shugaban Amurka mai ci yanzu, Barack Obama dan jam’iyar Democrat, yana karanta littafin da aka rubuta kan tarihin rayuwar Mr. Reagan
Amurkawa suna bukin cika shekaru dari da haihuwar tsohon shugaban kasar Ronald Reagan wanda yake da kwarjini a kasar inun.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024