Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Goyon Bayan Canji A Masar Cikin Tsanaki


Zauren taron kan harkokin tsaro da ake yi a Munich a Berlin.
Zauren taron kan harkokin tsaro da ake yi a Munich a Berlin.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta bayyana goyon bayanta ga shirin mika mulki cikin tsari a Masar,karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Omar Suleiman.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta bayyana goyon bayanta ga shirin mika mulki cikin tsari a Masar,karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar, Omar Suleiman,amma manzon Amurkan na musamman zuwa Masar,yace tilas Mubarak ya ci gaba da zama shugaban kasar yayinda ake mika mulki.

Manzon Amurkan Frank Wisner,ya gayawa wani taron gameda harkokin tsaro da ake yi a Munich jiya Asabar,cewa ana bukatar Mr. Mubarak ya jagoranci canji da ake nema a kasar.Da yake magana ta na’urar vidiyo ga taron,Wisner,yace rawar da Mubarak zai taka tana da muhimmanci.Amma daga bisani,MHWA ta tsame Kanta daga kalaman Mr wisner,tana cewa yana magana ne a matsayinsa na dan kasa ba kakakin gwamnati ba.

Cikin kalamanta a taron,Clinton ta jaddada cewa aiwatar da canji cikin lumana zai dauki lokaci,ta kara da cewa, “manufofin a bayyane suke”.Amma akwai kalubale kan bayanan aiwatar dasu.

Jiya Asabar,mataimakin shugaban kasar Omar Suleiman ya tattauna da wakilan ‘yan hamayya domin duba yi yuwar kafa gwamnatin wucin gadi karkashin jagorancinsa.

Shugabar Jamus Angela Merkel, ta fada a Munich tace za’a sami canji a Masar,kuma akwai bukatar a yi haka cikin lumana.Shi ma da yake magana PM Ingila David Cameroon yace babu dai-daito a halin yanzu a Masar,kuma ba za’a sami haka sai an aiwatar da sauyi.

Haka ma a jiya Asabar,ministan harkokin wajen Masar, Aboul Gheit ya soki shugaban malaman Iran Ayatollahi Ali Khameini,bayan yace gwagwarmayar da ake yi a Masar masu neman ‘yancin islama ne.Ministan yace tilas Ayatolahin ya fi maida hankali kan hankoron jama’ar kasarsa dake neman ‘yanci mai makon neman kauda hankalinsu gameda abinda ke faruwa a Masar.

XS
SM
MD
LG