Biyo bayan wani farmaki ta sama akan taron wasu masu halartar wata jana’iza, inda har aka hallaka sama da mutane 140 a birnin Sana’a kuma akalla mutane 500 suka jikata.
A wata sanarwa da yammacin Asabar, kakakin majalisar tsaron Amurka, Ned Price, yace Amurka tana bakin cikin ainun a kan wannan farmakin a kan mutanen dake halartar jana’izar, abinda ke nuna ci gaban karin kai irin wadanan hare haren a kan fararen hula a Yemen.
Ita ma gweamnatin Saudiyya ta fada a jiya Lahadi cewa zata kaddamar da nata bincike akan yadda wannan al’amarin ya faru.
Izuwa yanzu babu wani cikakken bayani a kan abubuwan dake kunshe a cikin wannan farmakin. Amma dai rahotannin sun nuna cewa ma’aikatar agaji sun yi amfani da buhuhuna suna tattara gabobin daruruwan mutane da suka tarwatse a wannan farmakin a nan zauren zaman makokin da kuma wajen ginin.
Akasarin wadanda sukabada bayanai gameda wannan harin sun ce anyi asaran rayukkan ne a sanadin wani roka mai linzame da wani daga cikin jiragen saman yakin ya cillo ne, kuma wannan shine farmaki mafi yin barna tun lokacin da Saudiya ta fara wannan yaki a Yemen a cikin watan Maris 2015.
Hukumomin Saudi Arabia dai sun musunta cewar suna da hannu a wannan harin, koda yake wani rahoto yace mai yiyuwa ne ba za’a rasa hannun ‘yan kunar bakin wake a cikin wannan harin.