Wasu kafofi biyun sun sheda wa V-O-A cewa Amurka na shirin aikawa da wani jibgegen jirgin ruwa dake dauke da tarin jiragen saman yaki zuwa yammacin tekun Pacific a wani mataki da ake ganin kamar karin jan kunnen Koriya ta Arewa (KTA) ne akan ta shiga hayyacinta dangane da yawan gwaje-gwajen da take yi na makamanta masu linzami.
Yanzu wannan jirgin na uku na USS Nimitz, wanda daya ne daga cikin jiragen ruwan jigilar jiragen sama mafi girma a duk duniya, zai je ne can ya tare da sauran manyan jiragen ruwa biyu irinsa da suka hada da USS Carl Vinson da kuma USS Ronald Reagan, wadanda yanzu haka suna can cikin tekun na Pacific.
Wannan matakin yana da muhimmanci idan akayi la’akari da cewa ba safai Amurka ke fita da irin wadanan jiragen ruwan har guda uku a lokaci guda zuwa wani yanki na duniya guda shi kadai ba.
Sai dai kuma yawan gwajin makamanta masu linzame da Koriya ta Aerewa ke ta yi akwanan nan, ance ya na damun gwamnatin Amurka ainun, abinda yassa shi kuma shugaban Amurka din Donald Trump ya lashi takobin cewa ba zai kyale Koriya ta Arewa ta iya samun makamin da zai iya kaiwa ga Amurka ba idan an harbo shi daga can, koda yake kuma masana sunce mai yiyuwa ne kafin shekarar 2020 Koriya ta Arewa, ta sami fasahar kera irin wannan rokan.
Facebook Forum