Kafin wannan muhimmin zabe na farko a kakar zaben ta bana, kuri’un neman ra’ayoyin jama’a a jihar ta Iowa sun nuna cewa a tsakanin manyan jam’iyyun Republican da Democrat, babu wani fitaccen gwani, inda ‘yan bana-na-shigo a harkokin siyasar jam’iyyun biyu suke ci gaba da nuna kasaita.

A bangaren ‘yan Republican, attajiri Donald Trump ya bayar da rata marar yawa ma sanata Ted Cruz daga Jihar Texas, wanda alamu suka nuna cewa yayi tuntube a lokuta da dama kafin wannan zabe nay au.
A bangaren ‘yan Democrat kuwa, zaben kusan ya zamo na kan mai uwa da wabi a tsakanin tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton, da sanata dan Indipenda daga Jihar Vermont, Bernie Sanders, wanda ya ayyana kansa a zaman dan Democrat mai ra’ayin gurguzu.
Masu kwadayin tsayawa takarar sun karade jihar ta Iowa jiya lahadi, suka gudanar da tarurruka a kowane lungu na jihar, tare da caccakar lamirin abokan adawarsu.