WASHINGTON, DC —
Da yake bayyana cewa wannan “ba kuduri ne da aka dauka a saukake ba,” kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, John Kirby yace ba abinda Amurka bata yi ban a ganin cewa wannan yarjejeniyar tayi anfani, amma, a cewashi, “Rasha ta ki ta cika nata aiki” da ya shafi yarjejeniyar.
Kakakin yace Rasha ta kasa, ko kuma taki, ta matsawa gwamnatin Syria lambar tayi aiki da sharuddan dake kunshe a yarjejeniyar wadanda Rashar ta aminta da su, a maimakon haka, Rasha ta zabi yin anfani da karfin soja kawai.
To amma Rasha ta musanta wannan ikrarin na Amurka, inda jakadanta a MDD Vitaly Churkin yake cewa “in ba don Rasha ba, da yanzu ko ina ba abinda ake gani illa tutucin kungiyar mayakan ISIS ko ina a cikin Damascus, babban birnin kasar ta Syria.”