Kafafen labaran Amurka na cewa jami’ai sun yi imanin cewa Sayoc yana aika sakonnin ne zuwa da mutanen dake cikin jerin sunayensa, wanda kafar labarai ta NBC ta ce ciki har da ‘yan jarida da ‘yan wasan nishadantarwa, lokacin da aka kama shi a makon da ya gabata.
Ana zarginsa da aika sakonnin bama bamai ga mutanen da suka hada da tsohon shugaban Amurka Barack Obama da mataimakinsa Joe Biden, wanda ake kyautata tsammanin zai yi takara a zaben 2020 da kuma tsohuwar abokiyar hamayyar Trump a zaben 2016 Hillary Clinton da wasu tsoffin manyan jami’an tsaro biyu.
Sayok mai shekaru 56 a duniya, Jiya Litinin a karon farko ya bayyana gaban kotu a Miami ta jihar Florida.
Facebook Forum