Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Barazanar Daina Ba Hukumar WHO Kudade


Amurka zata dakatar da bada kudade ga hukumar lafiya ta duniya ta WHO, inji shugaba Donald Trump, a cewarsa hukumar bata fahimci al'amarin yaduwar cutar COVID-19 ba.

Trump da jami’an gwamantinsa sun zargi hukumar ta kasa-da-kasa da nuna banbanci da kuma fifita China, kasar da cutar coronavirus ta fara bulla.

“Hukumar bata cimma burin da ya kamata ta cimma ba, a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo dake tsaye a gefen Shugaba Trump ranar Laraba 8 ga watan Afirilu, a lokacin wani taron manema labarai na kwamitin fadar White House dake sa ido akan cutar coronavirus. Muna sake nazarin kudaden da muke ba hukumar WHO, a cewar Pompeo.

Shugaba Trump ya ce gwamnatinsa zata gudanar da bincike akan hukumar kafin ta yanke shawara akan kudaden da zata bata nan gaba, hukumar na samun miliyoyin kudade daga gwamnatin Amurka a duk shekara.

Wannan shine kwana na biyu a jere da shugaban kasar ke caccakar hukumar ta WHO da kuma barazanar dakatar da bada tallafin kudade daga gwamnatinsa, wadda ita ce babbar mai tallafa wa hukumar ta musamman ta Majalisar Dinkin Duniya.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya da hukumar WHO sun yi watsi da barazanar da shugaba Trump ya yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG