Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Alkawarin Dalar Miliyan 50 Domin Tallafawa Mata A Afirka


 Donald Trump da Angela Merkel
Donald Trump da Angela Merkel

Taron kasashe masu karfin tatattalin arziki a cikin mahawararsu harda batun yadda za a hada kai da kasashen Afirka wajan tinkarar batun bakin haure da kiwon lafiya.

A yau aka shiga rana ta karshe ta taron kolin kungiyar kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya, watau G-20, a yayin da zanga-zangar nuna kyamar taron ke karuwa, kuma a yayin da shugaba Donald Trump na Amurka ke mamaye ajandar taron kolin.

A gefen wannan taro, shugaban na Amurka ya gana da shugabannin Britaniya, Indonesiya, Singapore, Japan, da kuma China.

Har ila yau, Trump ya shiga tattaunawar da aka yi kan hada kai da kasashen Afirka wajen tinkarar batutuwan kaurar bakin haure da kiwon lafiya, ya kuma bi sahun shugabanni wajen shiga wani taro kan mata ‘yan kasuwa a inda yace Amurka zata yi alkawarin dala miliyan 50 ga Shirin tallafawa Mata da Kudi don bunkasa Sana’o’insu, shirin da MDD ke gudanarwa, kuma diyarsa Ivanka take goyon baya.

Sai dai kuma babban abinda ya fi jan hankali a wajen taron kolin na kwanaki biyu shine zaman da Trump yayi da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, jiya jumma’a. Da alamun shugabannin biyu sun yi ganawa mai gamsarwa ta tsawon awa biyu da wani abu, har ma ta kai sai da shugaba Trump ya dage ganawar da ya shirya da firayim minister Theresa May ta Britaniya zuwa yau asabar a saboda sun shiga cikin lokacin wannan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG