Matakan hadin gwiwa na Amurka da kungiyar Tarayyar Turai, wani bangare ne na hobbasar da ake yi a matakin kasa da kasa na ladabtar da gwamnatin Assad saboda saba ma dadaddiyar ka'idar kasa da kasa ta hana amfani da makamai masu guba," a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, Heather Nauert.
Jami'ai 16 da aka kakaba ma takunkumin an hana su shiga Turai, kuma za a kwace kaddarorinsu da ke Turai.
Ministan Harkokin Wajen Burtaniya, ya bayyana matakin da kungiyar ta EU ta dauka jiya Litini a matsayin mataki mai kyau sannan ya kara da cewa ya yi farin cikin ganin Ministocin sun hada kai wajen maida hankali kan wannan batun.
Majalisar dinkin duniya da Hukumar Hana Amfani da makamai masu guba na gudanar da bincike na bai daya kan harin da aka kai a watan Afirilu da iskar sarin a Khan Sheikhun da ke Siriya, wanda da hallaka mutane akalla 87.
A hotunan bidiyon harin har akwai inda ke nuna yara na fitar da kumfa ta baka, kuma su na numfashi da kyar.
Facebook Forum