Hukumomin jihar Arizona sun tabbatar da mutuwar mutane tara bayan da bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa wani wurin shakatawa.
Ambaliyar ta afkawa wata korama dake yankin kogin da ake kira Verde a cikin wani gandun daji, mai tazarar kilomita 145, daga arewa maso gabashin birnin Phoenix.
Kuma babu wata alama da ta gargadi mutanen kafin bangon ruwan ya afka masu kamara yadda bayanai suka nuna.
"Ba tare da wani gargadi ba, suka ji amon ruwa, kamin kace kobo ruwan ya rufe su," In ji Ron Settelmaier, shugaban 'yan kwana-kwana a yankin.
Masu aikin ceto sun gano gawarwakin mutane uku a ranar Asabar,sannan suka kara tsinto wasu shida jiya Lahadi, sun kuma ba da labarin cewa har yanzu ba'a ga wani yaro dan shekaru 13 da haifuwa ba.
Facebook Forum