Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tsaurara Matakan Bada Izinin Zama Kasar


Donald Trump
Donald Trump

Gwamnatin Trump ta yi shelar bullo da wani tsari jiya Litini, wanda zai hana bakin hauren da ke cikin kasar samun takardar zama dindindin ko ta zama dan kasa, muddun sun dogara ne ga taimakon gwamnati, irin na kiwon lafiya, da abinci ko kuma muhalli.

Ken Cuccinelli, mukaddashin shugaban hukumar shigi da fici da kuma bayar da takardar shaidar zama dan kasa, ya yi shelar abin da ya kira, “Tsarin Hana Shigowa Amurka Don a Dogara ga Tallafin Gwamnati,” wanda, a ta bakinsa, “zai karfafa gwiwar masu niyyar shigowa, ko ci gaba da zama Amurka, su yi shirin tashi su nemi na kansu, su kuma zama masu dogaro da kai.”

Sabon tsarin zai fara aiki ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 2019. A karkashin tsarin, an fassara wanda ya zama nawaya ga gwamnati da wanda ya amfana da wani, ko wasu, tallafi na gwamnati na tsawon watanni sama da 12 a tsawon watanni 36. A karkashin wannan tsarin, za a kirga karbar tallafi sau biyu a wata guda a matsayin watanni biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG