A cikin gaisuwar da Amurka ta aika ta bakin sakataren harkokin wajen kasar John Kerry ta gaida Najeriya da cika shekaru hamsin da shida da samun 'yancin kai.
John Kerry yace a madadain shugaban Amurka Barack Obama da al'ummar Amurka ya sake jaddada karfin gwuiwar da yake dashi cewa Najeriya tana aiki tukuru domin ta warware kalubalen da take fuskanta yanzu.
Yace "kwana kwanan nan na dawo daga ziyara ta ukku zuwa Najeriya a matasyina na kasancewa sakataren harkokin wajen Amurka kuma na samu kwakwarar shaida cewa kasar ta kuduri aniyar gina Najeriya mafi kyau da daraja da kasashen duniya zasu dinga jinjina ma."
Ya cigaba da cewa "lokacin ziyarar an tunsheni cewa 'yan Najeriya da dama suna kokarin hada kawunan mutanen kasar da al'adu da addini da kabilanci suka raba kawunansu. Akwai sauran aiki tukuru da za'a yi saboda ba kowa damar damawa cikin tattalin arzikin kasar da kawo karshen cin hanci da rashawa da cin nasara kan kungiyar Boko Haram. Kazalika yakamata a mutunta hakkin kowa tare da baiwa mutanen dake gudun hijira tallafi".
Mun san 'yan Najeriya na matukar kokarin shawo kan duk kalubalen da kasar ke fuskanta, inji John Kerry.
Amurka na hankoron ganin an karfafa dangantaka da zumunci da duk 'yan Najeriya domin mu yi aiki tare saboda cigaban Najeriya da ma Afirka gaba daya a cewar John Kerry.
Ya kare da cewa "Muna yi maku fatan alheri a wannan bikin cika shekaru hamsin da shida da samun 'yancin kai.