Idan kuwa har suka rage din, wannan ne zai zama karo na farko da kungiyar ta tsayar da irin wannan shawara a cikin shekaru takwas.
Ba a bayyana tushen wa’yannan labaran ba dake cewar kasashen OPEC din zasu rage kadan ne a cikin abin da suke samarwa, daga ganguna miliyon 33 zuwaganguna milyan 32 da dubu dari biyar a duk rana. Kungiyar OPEC dai take samr da sulusi daya na dukkan man da ake sha a duniya.
Parashin mai ya taba haura dollar dari ganga guda, amma daga bisani sai ya rika fadiwa musamman a shekarar 2014 inda samar da mai ya inganta ayyuka a Amurka.
A da, idan aka samu fadiwar parashin mai, kasashen OPEC suna daukar shawarar rage samar da mai wanda ke haifar da tashin parashin. Saudi Arabia dake taka muhimmiyar rawa a harkar OPEC itace tafi hanzari wajen saurin rage man da take sarrafawa.
Amma a ‘yan kwannakin nan hukumomin na Saudiya sun ce ba zasu kara rage mansu ba har sai sauran kasashen dake cikin OPEC su kuma sun biyo sawu, sun rage nasu man, abinda yassa yawan man ya ci gaba da karuwa a kasuwanni amma farashinsa na ci gaba da foduwa warwas a kasa.