Amurka ta iza keyar tsohon shugaban kasar Panama Ricardo Alberto Martinelli zuwa Panama domin ayi masa shari’ar bisa zarge zargen almubazaranci da leken asirin cikin gida.
A watan Disamban shekara ta dubu biyu da goma sha biyar kasar Panama ta gabatar da umarnin kama tsohon shugaban. Yana zaune ne a Coral Gables jihar Florida nan Amurka.
Tsohon shugaba Martinelli yaja ragamar mulkin Panama daga shekara ta dubu biyu da tara zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.
Ana cajin sa ne da laifin amfani da na’urar sauraron maganganun mutane dari da hamsin ta wayarsa ta hannu da na’uarar computa, ciki harda abokansa yan siyasa da masu hamaiya da ma’aikatan jakadancin Amurka da alkalai da kuma yan jarida.
Haka kuma ana zaton ya saci fiye da dala miliyan goma kudin jama’a.
Facebook Forum