Wani kakaki a fadar Eric Schultz, yace irin wannan tariya, ta ci karo da burin da Rasha ta bayyana cewa tana kokarin tsara canjin shugabanci a Syria.
Shultz yace kada fa a manta Assad shugaba ne wanda yayi amfani da makamai masu guba kan jama'arsa, kuma farmakin da Rasha take kaiwa kan 'yan tawaye wadanda suke fafatawa da sojojin Syria ba zai haifi da mai ido ba.
Jami'an Amurka suka ce ziyarar da shugaba Assad ya kai Mosco baizo musu da mamaki ba, duk da cewa fadar shugaban kasar ta Kremlin ta boye labarin ziyarar.
An hakikance cewa wannan itace ziyara ta farko da Shugaba Assad ya kai wata kasar wace tun shekara ta 2011,lokacinda zanga zanga cikin lumana na nuna kiyayya kan gwamnatin kasar ta fara girma har ta zama yakin basasar da kasar take fama dashi ahalin yanzu. Zuwa yanzu dai rikicin ya kashe akalla mutane dubu metan da arba'in,galibinsu farar hula.
Shugaba Assad yayi shawarwari da shugaba Vladimir Putin a fadar Kremlin. Ya godewa shugaba Putin saboda katsalandan da yayi cikin rikicin kasar, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen hana bazuwar "karin ta'addanci" a Syria. Ta'adda itace kalamar da shugaba Assad yake amfani da ita wajen ambaton 'yan tawayen kasar.