A Pakistan ana zargin cewa ‘yan sanda sun yi awon gaba da daruruwan magoya bayan tsohon Firai ministan kasar Nawaz Shariff, kwana guda kafin ya koma kasar tare da ‘yarsa Maryam Shariff, wacce ake ganin ita za ta gaje shi fagen siyasa, yayin kuma da dukkansu ke fuskantar yiwuwar a tsare su.
Mambobin jam’iyyar Shariff ta League-N ko kuma (PML-N) a takaice, ta ce kamen dumbin magoya bayanta da aka yi, yunkuri ne na hana ba Shariff kyakkyawar tarba a Lahore, inda zai isa a yau Juma’a tare da ‘yarsa a wani jirgin fasinja.
Hukumomi a Lardin Punjab, sun ce ba su ba da izinin a kama kowa ba, amma wasu rahotanni sun ruwaito cewa, ‘yan sandan sun dauki matakin kamen ne, saboda a kaucewa tashin hankali a birnin, gabanin isowar Shariff.
A ranar Juma’ar da ta gabata, wata kotun da ke yaki da cin hanci da rashawa ta yankewa Shariff hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru goma, ‘yarsa kuma shekaru bakwai a wani zaman kotu da ba su halarta ba, bayan da suka gaza yin bayani kan yadda suka mallaki kadarori masu tsada a London.
Shi dai Shariff na zaune ne a London da ‘ya’yansa, inda yake jinyar matarsa wacce ke karban magani, saboda cutar daji ko kuma Cancer da take fama da ita.
Facebook Forum