Shugaban Amurka Donald Trump, ya ayyana dokar ta-baci sanadiyyar cutar coronavirus a kasar, matakin da zai samar da kudade ga jihohi da biranen kasar domin yakar wannan annoba.
Yayin wani taron manema labarai a jiya Juma'a, wanda aka watsa kai-tsaye ta talbijin a Fadar White House, Trump ya ce “Amurka za ta shawo kan wannan barazana.”
Shugaba Trump wanda a baya ya taba ayyana dokar ta baci har sau biyar, na fuskantar matsin lamba a ‘yan kwanakin nan, musamman daga ‘yan Democrat, wadanda suka yi ta kiran da ya dauki irin wannan mataki.
Sukar na zuwa ne yayin da gwamnoni da Magadan Gari suke ta ayyana dokar ta-bacin a yankunansu, inda aka soke duk wasu taruka tare da rufe makarantu.
“Irin illar da Trump ya yi ga kimarmu da dangantakarmu da kawayenmu, ta shafi dabarar da muke da ita ta tunkarar wannan annoba da ta addabi duniya," a cewar dan takarar mukamin shugaban kasar Joe Biden kenan yake cewa.
Sai dai matakin ayyana dokar ta-bacin, zai samar da biliyoyin daloli wadanda za a yi amfani da su a matsayin tallafi ga jihohin kasar.
Tasirin Dokar Ta-Baci Kan Kasuwannin Hannayen Jari
Tuni dai kasuwannin hannayen jari suka fara farfadowa a nan Amurka, bayan da Shugaba Trump din ya ayyana dokar ta-bacin sanadiyyar cutar ta COVID-19.
Sai dai duk haka, wasu alkaluma na nan kamar yadda suka fuskanci tawaya a wannan mako.
Kasuwar Dow Jones ta tashi da maki 2,000 a jiya Juma’a, wato daya daga cikin ranaku mafiya kyawu da kasuwar ta gani.
Kasuwar S&P ita kuma ta tashi da kashi 9.3 yayin da ta kere-keren fasohohin zamani ta Nasdaq ta tashi da 9.4.
A can nahiyar Turai ma, an rufe kasuwar hannayen jarin ne da kafar dama, amma duk da haka, tasirin bai yi wani abin a zo a gani ba ga irin illar da cutar coronavirus ta yi ga kasuwar.
Sai dai a nahiyar Asiya, kasuwar hannayen jarin faduwa ta yi warwas saboda rige-rigen sayar da hannayen jarin da aka yi.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da unguwar hada-hadar kudade ta Wall Street ta yi faduwar da ba a taba gani ba tun bayan shekarar 1987.