A yau Talata Shugaban Amurka Donald Trump da Firai Ministan India Narendra Modi suka ce suna aiki kan wata yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu, bayan da suka yi wata tattaunawa a birnin New Delhi, a rana ta karshe da Trump yake ziyarar aiki a kasar.
Ya ce, “Firai minista Modi na yin huldar kasuwancinsa da tsafta. Tawagoginmu suna samun ci gaba a kokarin da ake yi na kulla wata yarjejeniyar kasuwanci".
Gabanin haka, Shugaba Trump ya bayyana wata yarjejeniyar sayar da makamai da suka kulla da Indiyan, inda Amurka za ta sayar wa da dakarunta jirage masu saukar ungulu da wasu makamai, wadanda kudadensu suka kai dala biliyan uku.
Shi dai Shugaba Trump ya kwatanta dangatakar da ke tsakanin Amurka da India a matsayin “wacce ta kara kyautatuwa fiye da.”
Shi ma dai Firai Minista Modi, ya jinjina dangatakar Amurka da kasarsa, wacce ya ce ta kai wani muhimmin matakin da ba ta taba kai wa ba.
Facebook Forum