Amurka da China, manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya, sun fara wata tattaunawa a fannin cinikayya yau Laraba a Washington, domin rage gibin cinikayya na dala biliyan dari uku da tara da aka samu bara da Beijing.
Yayinda aka fara tattaunawar, sakataren ma'aikatar cinikayya Wilbert Ross ya shaidawa mataimakin shugaban kasar China Wang Yang cewa, “tilas ne mu kara samun daidaito a cinikayyarmu, mu kara yawan kayan da muke sayarwa da aka sarrafa a Amurka zuwa China. Akwai dama sosai ta yin haka idan zamu yi aiki tare mu kawar da shingen dake akwai.
A nasa bangaren, Wang yace cinikayya tsakanin kasashen biyu mai yiwuwa ce, sai dai ya yi gargadi da cewa, sa in sa nan da nan zai iya dagulawa kowanne bangare lissafi.
Sakataren ma'aikatar kudin Amurka Steve Mnuchin yace za a iya samun cin moriyar huldar cinikayya ne kawai idan ana mutunta juna .
Facebook Forum