Rahotanni sun bayyana cewa Amurka ta yi watsi da kiran da kasashen Turai kawayenta suka yi gareta, akan a fidda su daga takunkumin da Amurka din ta sanyawa kasashen dake harkokin kasuwanci da Iran.
A cewar jami’an diplomasiyya da wasu kafofin gwamnati, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo da sakataren baitulmanin Amurka Steven Mnuchin sun rubuta wata wasika zuwa ga Burtaniyya, da Faransa, da Jamus akan cewa Amurka ba zata bada kariya ga kasashen dake yin huldar kasuwanci da Iran ba.
“Pompeo da Mnuchin sun fada a wasikarsu, da gidan talabijin din NBC ya bada rahoto akai, cewa suna neman su sanya takunkumin toshe hanyoyin samun kudade da ba a taba sanyawa ba a baya akan gwamnatin Iran.”
Sai dai kuma, Amurka ta ce zata rage wasu daga cikin matakan a bisa ga dalilan tsaron kasa da kuma bukatar bada taimakon agaji ga masu bukata.
Wannan wasikar dai maida murtani ne ga bukatar da Burtaniyya, da Faransa, da Jamus suka gabatar a watan da ya gabata.
Facebook Forum