Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Ta Tsallake Matakin Farko Na Barkewar COVID - 19 Ba - Fauci


Dr Anthony Fauci
Dr Anthony Fauci

Yayin da wasu kwararru a fannin lafiya ke gargadin cewa mai yiwuwa a kuma samun barkewar cutar COVID-19 a karo na biyu, wasu na cewa Amurka da wasu sassan duniya ba su tsallake matakin farko na barkewar cutar ba.

Kwararren Likitan Amurka a fannin ilimin cututtuka masu yaduwa Dr. Anthony Fauci ya ce, “ta ya ya za a rika maganar samun barkewar cutar a karo na biyu, bayan ana samun mutum dubu 20 da ke kamuwa da cutar a kullum.”

Mafi aksarin yankunan Amurka sun fara sassauta matakan dakile yaduwar cutar da aka saka, yayin da adadin masu harbuwa da ita ke karuwa a wasu jihohi musamman na Kudanci da Yammaci.

Wasu daga cikin kwararru a fannin kiwon lafiya irinsu Caitlin Rivers, wacce ke bincike a John Hopkins ta ce, kuskure ne a ma rika cewa za a samu barkewar cutar a karo na biyu, domin a cewarta hakan, zai rika sa mutane suna tunanin an wuce mataki mafi muni a yaduwar da cutar ke yi.

Ita dai Amurka wacce ke da mutum sama da miliyan 2.2 da suka kamu da cutar, ta kasance kasar da ta fi yawan wadanda cutar ta harba a duniya.

Har ila yau Amurkan ce dai ke kan gaba a yawan wadanda suka mutu sanadiyyar wannan annoba ta COVID-19.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG