Ranar Alhamis 18 ga watan Yuni kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa gwamnatin Trump ba za ta iya soke shirin nan da ake kira DACA a takaice ba, wato shirin da ya kare yara bakin haure akalla 650,000 da ke Amurka daga maida su kasashensu na asali.
Babban Alkali Mai ra'ayin ‘yan mazan jiya, John G. Roberts, ya hade da alkalan kotun guda hudu masu sassaucin ra'ayi inda su 5 suka goyi bayan taka wa gwamnatin Trump burki 4 kuma suka yi akasin haka.
Ana kallon hukuncin kotun a matsayin wani koma baya ga Shugaba Donald Trump, wanda ya nemi ya dakatar da shirin na DACA tun shekaru biyu da suka gabata. Shirin dai ya kare baki marasa takardun izinin zama a Amurka, wadanda aka kawo su kasar tun suna yara, ko da ya ke yawancinsu sun girmi yanzu.
Tsohon Shugaban kasa Barack Obama ne ya kirkiri shirin a shekarar 2012 don samar da kariya ga matasa baki da suka cancanta, ta yadda zasu samu damar zama a kasar su kuma iya yin aiki da zuwa makaranta.
Facebook Forum