A washegarin fitar da sakamakon zaben da ya bayyana Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara a zagaye na 2 na zaben shugaban kasar Nijar ne hukumomi suka kama shugaban kungiyar MDC Anas Djibrilla wanda bayan shafe sa'o'i 48 a ofishin ‘yan sandan farin kaya aka wuce da shi zuwa gidan yarin Koutoukalle.
Sai dai zancen da ake lauyan da ke kare shi bai sami ganinsa ba ballantana a yi masa shara’a, saboda haka kungiyar Amnesty International ta bukaci hukumomi su sallame shi ko kuma su gabatar da shi ga alkali domin a yi masa shari’a.
Anas wanda tsohon shugaban kungiyar daliban jami’ar Yamai ne na fama da rashin lafiya a cewar wasu majiyoyi abinda ya sa lauyan dake kare shi ya bukaci a bada belinsa a makon jiya sai dai kotu tayi watsi da wannan bukata.
Kakakin gwamnatin Nijar Tidjani Abdoulkadri da muka tuntuba akan wannan batu ya ce kawo yanzu bai sami kofin wannan wasika ta Amnesty ba, amma shugaban kungiyar RJRN mai da’awar kare manufofin gwamnatin Renaissance Anda Garba Moussa ya ce maganar Anas Djibrilla wani abu ne da tun tuni ya shiga kunnuwan shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Kwana 1 bayan da kotun tsarin mulkin kasa ta tabbatar da nasarar dan takarar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed a zaben da ya gabata an yi ta yada muryar Anas jibrilla ta manhajar whats’app yana cewa jama’a ta fito a Yamai da dukkan manyan biranen kasar nan domin kalubalantar wannan sakamako abinda ya sa kungiyar Amnesty ke ganin an fake ne da dokar hukunta masu laifika ta yanar gizo wajen kama shugaban na kungiyar MDC debout Nijar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: