Yayin da ake ganin babu tabbas ga komawa bisa teburin sasantawar, kwararru na ganin goyon bayan China akan wannan kokari yana da muhimmanci. To sai dai kuma abin tambaya anan shine, ko China za ta goyi bayan matakan da ake shirin ‘daukawa kan Koriya ta Arewar.
Kwararru a China sun ce gwamnatin kasar na iya bakin kokarinta don ganin ta taka wa Koriya arewa burki. A farkon shekarar nan China ta rage yawan gawayin Kwal da ake shigowa da shi kasar daga Koriya ta Arewa, haka kuna ta kara tsuke hanyoyin hada-hadar kudade zuwa Koriya ta Arewar.
Lu Chao, dake zaman wani babban malami ‘dan asalin Koriya ta Arewa, da yanzu haka ke koyarwa a wata makarantar kimiyya dake Arewa maso Gabashin China, ya ce duk bankunan kasar China sun dakatar da harkokinsu da bankunan Koriya ta Arewa.
Facebook Forum