Masu manufar kere-kere suna kira da a kara samar da kudade, musamman ga mata, wadanda ke taka rawa wajen kawo sauyi ga harkokin noma.
Sama da wakilai da kungiyoyi 400 da ke aiki a fannin noma na Afirka suna birnin Nairobi na kasar Kenya, domin tattaunawa kan yadda za a inganta noman zamani da rayuwar manoma da tsarin abinci na nahiyar.
Shugabannin dai sun shafe ranakun Talata da Laraba suna tattaunawa kan bukatar karin kudade, wanda ke da matukar muhimmanci wajen yaki da yunwa da karancin abinci. A cikin shekarun da suka gabata, manoman Afirka sun yi fafatawa wajen samar da isasshen abinci da zai ciyar da nahiyar.
DigiCow na daya daga cikin kamfanonin fasaha a taron da ya ce yana da amsoshin matsalar. Kamfanin na Kenya yana ba manoma damar adana bayanai, da samar da hayar samun kudi da kuma tallace-tallace. Maureen Saitoti shine manajan alamar DigiCow kuma ya ce dandalin ya inganta rayuwar manoma akalla rabin miliyan.
Hada tsarin fasahar zamani zuwa samar da abinci yana taimaka wa manoma samun iri da taki da lamuni da kuma hana kwari da cututtuka a gonakinsu.
Fasahar Agri-tech tana taimakawa wajen isa ga kungiyoyin da kafafai ake damawa da su ba, gami da mata. Sieka Gatabaki ita ce darektan shirin na Mercy Corps AgriFin, wanda ke cikin kasashe 40 da ke aiki tare da masu samar da kayan aiki na zaamni don kara yawan aiki da samun kudin shiga ga kananan manoma.
A cewar rahoton Zuba Jari na AgTech na 2024, noma ya samar da kudi dala biliyan 1.6 a cikin shekaru goma da suka gabata. Sai dai masana sun ce kudaden da ake ba su a halin yanzu bai wadatar ba wajen biyan bukatu da ake samu a fannin.
Daraktan dabaru da ci gaba a Briter Bridges David Saunders ya ce tsarin samar da kudade ya samo asali ne don tinkarar matsalolin da manoma da masana'antar abinci ke fuskanta.
Dandalin Mu Tattauna