Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta juyewa jiya jumma'a a birnin Kano, ya haddasa ambaliyar da ta mamaye tituna da wasu gidaje a birnin Kano, birni mafi girma a yankin arewacin Najeriya.
Wakilin sashen Hausa, Mahmud Ibrahim Kwari, ya gane ma idanunsa yadda ruwan ya rika kwarara yana neman malale wata gada a Unguwar Kar-Ka-Sara, a titin Inuwa Dutse kusa da asibitin Koyarwa na malam Aminu Kano, inda aka fuskanci barazanar cewa ruwan yana iya malale gidaje.
Wannan ne karon farko da ruwan sama yake barazanar haddasa ambaliya da malale kusan dukkan unguwannin ciki da wajen birnin Kano a daminar bana.
Da ma dai hukumar kula da yanayi da ta ayyukan gaggawa a Najeriya sun yi kashedi game da yiwuwar fuskantar ambaliya a saboda yadda yanayin daminar bana ke bayyana da ruwa kamar da bakin kwarya.
Ga rahoton Mahmud Kwari daga Kano.