Hukumomi a Nijeriya sun ce ambaliyar ta kashe a kalla mutane 102 a sashen kudu maso yammacin kasar cikin satin da ya gabata.
Kungiyar Agaji ta Red Cross a Nijeriya t ace dururuwan mutane sun rasa gidajensu bayan da ambaliyar ruwa daga wata madatsar ruwa ta lalata gidaje a birnin Badun, mai tazarar kilomita 150 daga birnin Lagos da ke gaban teku. Ambaliyar ta kuma rusa gadoji uku a yankin.
Hukumomi sun ce rashin tsarin gine-ginen gidaje da kuma karanci ko kuma toshewar kwatamai kan kara hadarin ambaliyar ruwa a irin wadannan wuraren a Nijeriya.
A halin yanzu Nijeriya na dab da yin adabo da damana, wanda kan fara daga watan Mayu zuwa Satumba. Da ma hukumomi sun yi gargadi kan yiwuwar saman ruwan sama sosai a wannan shekarar.
Mummunar ambaliya a wannan kasar ta raba wajen mutane 500,000 da gidajensu a bara.