An kwashe mutane sama da 30,000 da ke zaune garin Manila babban birnin kasar Philippines, a wurin da wani tsauni ke ta tunbudin tanderu da ruwan toka da kuma tururi, tun bayan da ya yi amai a ranar Lahadi.
Masana ilimin kimiyya a cibiyar binciken karkashin kasa ta Philippines sun kara matakin gargadin zuwa 4, wanda ke nuna cewa fuskantar mummunan aman wuta cikin ‘yan sa’o’i zuwa kwanaki.
Shugaban cibiyar binciken karkashin kasa ta Philippine Renato Solidum ya ce, “cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, Tsaunin Taal ya ci gaba da aman tanderu inda mu ka yi ta ganin wasu al’amura biyu:
Na farko shi ne tunbudin tanderu; na biyu kuma garwayar ruwa da sauran abubuwan da ke fitowa a aman tanderun har ke cillawa sama da tsawon kilomita biyu da kuma tokar da ke baduwa a yamma da kudu maso yammacin tsaunin na Taal.”
Facebook Forum