Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aman Wutar Dutse Ya Rutsa Da ‘Yan Najeriya Sama Da 200 A Yankin Karibiya


Aman Wutar Dutse a Yankin Karibiya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:50 0:00

Aman Wutar Dutse a Yankin Karibiya

Masana kimiyya sun yi gargadin cewa, dutsen zai iya kai wa kwanaki ko ma makonni yana amayar da wutar.

Akalla ‘yan Najeriya sama da 200 ne suka makale a Tsibirin St. Vincent Grenadines da ke yankin Karibiya, bayan da aman wutar dutse ya lullube yankin kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Bayanai sun yi nuni da cewa mafi aksarin ‘yan Najeriyar da ke zaune a yankin dalibai ne da wadanda suka je yawon shakatawa.

Jama’ar da ke yankin da lamarin ya rutsa da su, sun yi ta yada aukuwar wannan ibtila’i a kafafen sada zumunta.

“Don Allah ku taya ‘yan uwana da addu’a da ke tsibirin St. Vincent a yankin Karibiya – aman wutar dutse ya barke.” In ji Odin mai shafin Twitter na @dinmom.

Aman dutsen ya fara ne a ranar Juma’a 9 ga watan Afrilu ya kuma rufe sararin samaniya tare da lullube titunan yankin da toka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Jakadan Najeriya a kasar ta St Vincent Grenadines, Levi Odoe yana kira ga hukumomin Najeriya da su kai wa 'yan kasarta dauki.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin Najeriyar ba su ce komai ba, kuma yunkurin jin ta bakin hukumar da ke kula da sha'anin 'yan Najeriya mazauna kasashen waje ya cutura.

Hukumar ba da agajin gaggawa a kasar St. Vincent Grenadines ta ce wannan, shi ne karo na biyu da dutsen yake furzar da wutar a rana guda, kamar yadda gidan talbijin na CNN ya ruwaito.

Yankin St. Vincent Grenadines
Yankin St. Vincent Grenadines

Rahotannin sun nuna cewa, turnukin tokar aman wutar ya yi tashin tsawon kilomita 4 ko mita 2.5 a sararin samaniya.

Babu dai rahotanni da ke nuna cewa an jikkata ko an tafka asarar dukiya yayin da aka fara kwashe jama’ar yankin a jiragen ruwa.

Kasashen Antigua da Guyana da ke makwabata da kasar, sun aika da taimakon kayayyaki tare da amincewa su bude kan iyakokinsu ga kusan mutun 16,000 da ake kokarin kwashewa a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Lokaci na karshe da dutsen ya yi irin wannan amai shi ne a shekarar 1979, yayin da kwararru ke gargadin cewa, dutsen zai iya kai wa kwanaki ko ma makonni yana fitar da wutar.

A shekarar 1902, irin wannan bala’i ya hallaka mutum kusan 1,600 a kasar ta St. Vincent Grenadines da ke yankin na Karibiya.

XS
SM
MD
LG