Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR ta sanar da nadin Alphonso Davies, dan wasan baya na hagu na kungiyar kwallon kafa ta FC Bayern Munich, kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Canada, a matsayin sabon Jakadanda zai rika yada manufofinta.
"Ina alfahari da shiga Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, a matsayina na Jakadan kwarai. Abin da na gani ya sa mun shaukin yin magana game da 'yan gudun hijirar, don ba da labarinsu da kuma taimakawa wajen kawo canji." Davies ya ce.
Filippo Grandi, Babban Kwamishinan 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya, lokacin da yake maraba da sabon Jakada, ya ce: "Alphonso Davies ya nuna jajircewa, da iya wasa, kuma muna matukar murna da kasancewar shi tare da mu.
Wasanni na da karfin gaske wajen hada zumunci, da warkarwa da kuma taimakawa wajen tsara makoma don a cikin aikin da muke yi da 'yan gudun hijirar muna ganin yau da kullun abin da sauye-sauye na motsa jiki ke iya kawowa a rayuwarsu.
Labarinsa na kansa, hazakarsa da kuma nasarar da ya samu a matsayinsa na kwararren dan wasan kwallon kafa, da kuma jajircewarsa wajen taimaka wa 'yan gudun hijirar, ba karamin tasiri ba ne. Ina maraba da shi da kuma fatan yin aiki tare da shi.
"An haife shi a sansanin 'yan gudun hijira a Ghana, ga iyayensa ‘yan asalin Liberia da suka guje wa yakin basasa a kasarsu, Davies ya gane wa idanunsa abin da ake nufi da zama dan gudun hijira:"
"Yayin da sansanin 'yan gudun hijirar ya bai wa iyayena matsuguni, wuri ne mai bayar da aminci ga iyalina lokacin da suka gudu daga yaƙi, galibi nakan yi tunanin inda zan kasance idan da na zauna a wurin, kuma ban ci gajiyar damar da na samu ba saboda sake tsugunar da ni.
Ba na tsammanin da na isa inda nake a yau. " An sake dawo da Davies da danginsa zuwa kasar Canada lokacin da yake da shekara biyar. A shekara 15, Davies ya fara buga kwallon kafa na kwararru, kuma bayan shekara daya ne ya fara buga wa kasarsa wasa. Ya zama dan wasa mafi karancin shekaru a kungiyar maza ta Canada. Yanzu yana da shekaru 20, Alphonso na da sha'awar tallafa wa aikin UNHCR da kuma amfani da karfin motsa jiki, don taimaka wa wadanda aka tilastawa gudu don gina kyakkyawar makoma:
"Ina son mutane su samu fahimta game da mahimmancin taimaka wa ‘yan gudun hijira, a duk inda suke, a sansanoni ko birane, a kasashe makwabta ko kasashen da aka sake tsugunar da su kamar Canada. 'Yan gudun hijirar na bukatar tallafinmu don su rayu, amma kuma samun ilimi da wasanni, don haka za su iya karfafa su kuma su bunkasa da gaske. "