Kungiyar Kumasi Asante Kotoko ta sabunta kawance da babban kamfanin makamashin nan na Goil. Kotoko ta shiga kawancen shekara daya da Goil, wanda zai inganta hidimarsa ga kulob din da kashi 66.5.
"Muna farin cikin bada sanarwar kulla kawancenmu da Goil na tsawon shekara daya, wanda za a iya sake sabuntawa," abin da kungiyar ta rubuta kenan a shafinta na Twittan.
Majalisar zartaswar kungiyar Ghana GHALCA a takaice ta yi wani taro mai kayatarwa, da ministan matasa da wasanin motsa jiki, Yusuf Mustapha, akan yadda za a karfafa samun taimakon kudi da zai tallafawa mambobi.
Taron ya ta'alaka ne akan yadda za a samar da kudin da gwamnati ta yi alkawari zata baiwa kungiyoyin kwallo a rukuni na daya, da kuma kungiyoyin mata, har ma da babbar kungiyar League ta kasar wato Premier League majalisar ta bayyana goyon bayanta ga sabon Ministan wasanni.
Dan wasan tsakiya Mubarak Wakaso, zai jagoranci Black Stars a karawarta na samun cancantar shiga gasar cin kofin Afrika ta 2021, a ranar Alhamis, dan wasan tsakiyar zai zama Kaftin, yayin da Ghana zata cashe da Afrika ta Kudu a filin wasa na FND dake Johanesburg.
Wakaso, zai daura damarar Kaftin, kasancewar Adre Ayew Thomas Partey da Richard Ofori duk ba su samun sukunin yin wannan wasan ba. Ayew da Partey za su samu damar yin wasa na biyu a ranar Lahadi 28, ga watan Maris shekarar 2021.
Amma dan wasa Richard Ofori, saboda raunin da ya samu, ba zai buga wasan ranar Lahadi ba.
Hukumar kwallon kasar Ghana ta zayyana shirye-shiryen tafiya mai kyau ga Black Stars a karawarta da Afrika ta Kudu don samun cancantar shiga gasar cin Kofin Afrika ta 2021.
Ghana za ta yi artabu da Bafana-Bafanaa a ranar wasa ta hudu a filin wasa na FNB da ke birnin Johanesburg.Tuni 'yan Black Stars suka bar kasar zuwa Afrika ta kudu a ranar Talata da dare.
Sun yi atisayi a filin da za a yi wasan yau Laraba, bayan an yi musu gwajin Covid 19.
Za su bar Afrika ta kudu zuwa gida Ghana bayan wasansu, don fara shiri kan wasansu na gaba, inda za su kara da kasar Sao Tome and Pricipe a zagayen karshe na wasannin ranar Lahadi 28 ga watan Maris 2021.
Ga labaran Ridwan Abbas a cikin sauti.