Kungiyar gwanmonin jihohin Arewacin Najeriya ta ce ta dauki matakin maida Almajirai zuwa jihohinsu na asali don samar wa yaran kyakkyawan kulawa, da kuma basu ingantacciyar rayuwa.
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya ce, sun lura da yadda yaran da ake turawa wasu garuruwa don karatun Allo, sukan bige ne da barace-barace akan tituna, wanda ya kasance hadarine ga rayuwarsu.
Lalong ya ce, wannan mataki da gwamnonin Arewacin Najeriya suka dauka shine daidai, kuma hakan zai baiwa gwamnonin jihohin damar basu ingantacciyar kulawar da ta dace. Ya ce, daga cikin Almajiran da aka dawo dasu jihar Plateau, an samu guda daya yana dauke da cutar coronavirus.
Barista Lawal Ishaq dake aiki da kungiyar Jama’atu Nasril Islam a jihar Plateau ya ce, sun yi na’am da matakin maida Almajiran gaban iyayensu. Ya ce, wannan matakin zai taimakawa yaran su samu ingantacciyar rayuwa.
Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Shabul Mazadu ya ce, tarbiyyar da yara za su samu daga iyayensu nada muhimmanci a rayuwarsu.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Zainab Babaji.
Facebook Forum