A shekara ta 2013 aka kama kuma aka tuhumi Alhassane Ould Mohammed, kan zargin kisan William Bultemeier, da kuma yunkurin kashe wani sojan Amurka, yayinda mutanen biyu suke barin wani wurin cin abinci a birnin Niamey, babban birnin kasar Nijar a shekara ta 2000.
Masu bincike suka ce Mohammed, mai inkiya Cheibani, da wani mutum sun tunkari Amurkawan biyu, suka nemi su basu makullin motarsu, mai lasin difilomasiyyar Amurka. Masu gabatar da kara suka ce mutanen biyu suka bude wuta kan Amurkawan, suka kashe Bulteimer, suka kuma raunata sojan-saje Christopher MCneely.
Bayan da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a Mali kan wannan laifi, sai ya tsere daga gidan fursina.
A 2013 ne dakarun faransa suka kama shi daga bisani suka mikashi ga Amurka.
Ahalinda ake ciki kuma,an kashe mutane 11, ciki harda sojoji takwas a wani barikin soja a Cape Verde.
Jami'ai a kasar dake a Afirka ta yamma suka ce, wani soja da ya bijire kuma yayi layar zana ne, ya kashe sojojin da fararen hula uku, ciki harda 'yan kasar Spain biyu.
Wata sanarwa da hukumomin kasar suka wallafa a shafinsu na internet sun danganta lamarin ga wani sabani ko dalili wanda bashi da nasaba da yunkurin juyin mulki, ko tarzoma da ake dangantawa da miyagun kwayoyi ba.