A hukuncin Kotun na jiya Laraba, ta yi amfani da dokar yadda ake kasafta dukiya, wacce ta ce za’a biya diyya ga iyalan sojojin ruwan Amurka guda 241 da aka hallaka a harin ta’addancin shekarar 1983 a birnin Beruit na kasar Lebanon.
Sai kuma wasunsu da suka mutu a harin shekarar 1996 akan tagwayen tulluwar Khobar a Saudiyya, dama wasu hare-hare makamantansu. Hukuncin da kotun ta yanke don yin adalci ga iyalan sojojin da suka mutu a wadannan hari da Iran ta dau nauyinsa.
Hukuncin da ita Iran ta nuna rashin amincewa da shi, wanda tuni Lauyoyin wadanda abin ya shafa suka bazama neman duk inda wata kadarar kasar ta Farisa ta ke a nan Amurka don kaiwa gareta.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka dai a jiya Laraba ta ce yanke hukuncin bai zo mata da bazata ba, kasancewar dama tuntuni gwamanti ta nuna goyon bayan maganar biyan diyyar ga iyalan wadanda abin ya shafa.