Don haka ne suka bukaci hukumomin kasar su dubi wannan al’amari tun kafin abin ya tsananta.
Lura da irin babbar barazanar da rayuwar jama’a ke fuskanta a yankin Agadez inda kamfanin CNPC na kasar China ke aiyukan hakar man fetur ya sa sarkin garin Lahari Mahamat Sanoussi tattaki zuwa nan birnin Yamai domin sanarda hukumomi halin da al’uma ke ciki kamar yadda ya bayyana a taron manema labarai na hadin gwiwa da kungiyar ROTAB.
Sarki Mahamat Sanoussi cikin harshen tubanci yace muna cikin mawuyacin hali saboda haka wasu suka fara kaura domin kiwo shine aikin da nuka fi dogaro akansa amma kuma dabobinmu suna ta mutuwa bas a samin sararin su yi kiwo saboda yadda ake ta jibge kayan aikin shimfida bututu.
Man fetur ba abin da ya kawo mana sai matsaloli ba makarantu ba asibiti ba ruwan sha kuma kamfanin china bai taba ba yaranmu aiki.
A cewar sarkin Lahari a zuwansa nan yamai ya shigar da takardu a wasu ofisoshi da suka hada da ma’aikatar man fetur, majalsar dokoki, ofishin babban jami’I mai kula da shiga tsakani amma shiru ba wata amsa mai gamsarwa. wannan ya sa shugaban kungiyar ROTAB mai fafitikar ganin an yi adalci a sha’anin ma’adanai Ali Idrissa jan hankulan mauhukunta a dubi wannan batu da idon rahama.
Sha’anin man fetur a nan Nijar wata haraka ce da masu fafitika ke gunaguni akanta sakamakon rashin samun cikeken bayanii akan yadda ake gudanar da ita.
A shekarar 2011 jamhuriyar Nijar ta fara sayar da man fetur dinta a kasuwa inda a kowace rana ake hako ganga 20000 daga rijiyoyin man Agadem dake yankin Diffa wadanda ake tacewa a matatar SORAZ dake Zinder.
Ganin yadda abubuwa ke tafiya kamar yadda ake bukata ya sa gwamnatin kasar hada gwiwa da hukumomin Jamhuriyar Benin don fitar da man zuwa kasuwannin duniya ta hanyar bututun da a yanzu ake gudanar da ayyukan shimfidawa.
Yunkurin jin ta bakin jami’ai a ma’aikatar man fetur dangane da irin wadanan korafe-korafe ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: