Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiyuwar ‘Yan Najeriya Miliyan 33 Su Fuskanci Matsalar Karancin Abinci A 2025 - Rahoto


Kayan abinci a kasuwar Najeriya
Kayan abinci a kasuwar Najeriya

Matsalar matsin tattalin arzikin da ake fama da ita da hauhawar farashi da tasirin sauyin yanayi da kuma ci gaba da tashe-tashen hankula a jihohin arewa maso gabashin Najeriya suka janyo karuwar hasashen.

Matsalar karancin abincin da Najeriya ke fama da ita za ta ta’azzara a 2025 kuma za ta jefa akalla ‘yan Najeriya miliyan 33 cikin yunwa.

Ana kiyasin cewa yawan jama’ar Najeriya a yau ya kai kimanin mutum miliyan 223.8.

Rahoton da kungiyar Cadre Harmonise’ ta fitar karkashin jagorancin gwamnatin Najeriyar da tallafin hukumomin bada agaji, ciki harda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi gargadi game da ta’azzarar matsalar karancin abinci a Najeriya, inda ake hasashen cewa kimanin mutane miliyan 33.1 zasu fuskanci matsanancin karancin abinci da kaka (tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025).

Bincike ya nuna cewa mutane miliyan 33.1 na wakiltar karin mutum miliyan 7 idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a bazarar bara.

Kayan abinci
Kayan abinci

Matsalar matsin tattalin arzikin da ake fama da ita da hauhawar farashi da tasirin sauyin yanayi da kuma ci gaba da tashe-tashen hankula a jihohin arewa maso gabashin Najeriya suka janyo karuwar hasashen.

A cewar rahoton, tsakanin watannin Oktoba da Disambar 2024, akwai yiyuwar kimanin mutane miliyan 25.1 su fuskanci matsalar karancin abinci, koda a ganiyar lokacin girbi ne.

Mutum miliyan 3.8 daga cikin mutanen na rayuwa ne a jihohin arewa maso gabashin Najeriya-adadin da ake hasashen zai karu da mutum miliyan 3 a 2025.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG