Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afurka Ta Ce Ta Zaburo Kan Batun Rigakafin Cutar Corona


Ginin Kungiyar Tarayyar Afurka da ke Habasha
Ginin Kungiyar Tarayyar Afurka da ke Habasha

Yayin da kowace nahiya a duniya ke bayyana irin matakan da ta ke daukawa wajen yaki da mugunyar cutar nan ta corona, Afurka ta ce ita ma ta himmantu ga wadata mutanenta da rigakafin cutar

Jami'ai a Afurka sun ce suna aiki don samo daruruwan miliyoyin alluran rigakafi ga nahiyar a cikin shekara mai zuwa, kuma suna kira a hada kai a Afurka a yakin da ake yi cutar coronavirus.

Nahiyar Afurka na da mutane miliyan 3.4 da aka tabbatar sun kamu da cutar tun farkon bullowarta a watan Fabrairun bara. Tun daga wannan lokacin, Dr. John Nkengasong ya ce cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin nahiyar sun gudanar da gwaje-gwaje har miliyan 30 - mafi yawansu a cikin kasashe 10, ciki har da Afurka ta Kudu, kasar da ta fi sauran kasashen Afurka fama da cutar ta coronavirus.

Kasashen Habasha, Najeriya, Kenya, Zambiya da Uganda, suma duk sun gudanar da gwajin.

Dakunan gwaje-gwaje ‘kasa da 500 ne kawai a fadin nahiyar ke gudanar da gwajin cutar. Nkengasong ya ambaci kasashe hudu da suka fara rigakafin cutar a kwanan nan, da suka hada da Maroko (Morocco) da Masar da Seychelles da kuma Guinea.

XS
SM
MD
LG